Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya sallami dukkan Sakatarorin Ilimi na kananan hukumomi 23 da ke fadin Jihar.
An sanar da hakan ne cikin wani sako da mashawarcin gwamnan na musamman kan harkokin sadarwa Muyewa Adekeye ya wallafa kan shafinsa na Twitter a ranar Talata.
- Fadar Shugaban Kasa ta fara nazarin sake rufe iyakokin Najeriya
- Buhari ya tsawaita aikin kwamitin COVID-19
Gwamnan ya kuma sauke Shugaban Hukumar Kula da Al’umma da Bunkasa Zamantakewa na Jihar (CSDA).
A madadin haka, gwamnan ya amince da nadin Saude Amina Atoyebi, Shugabar Ofishin zuba Jari ta jihar a matsayin mai rikon Hukumar ta CSDA.
Kazalika, ya nemi manyan jami’ai a kowace ma’aikatar ilimi da su yi aiki a matsayin sakatarori domin cike gurbin wadanda aka dakatar.
Ya ce matakin da aka dauka na sauke sakatarorin ilimin daga mukamansu wani bangare ne na sauya fasalin sasashen ilimi a jihar.