Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sallami mutum 19 daga cikin hadimansa a abin da gwamnatinsa ta kira rukunin farko na masu rike da mukaman siyasan da za a kora a aikin sallamar ma’aikatan da gwamnatin ke yi.
El-Rufai ya gamu da suka saboda korar dubban ma’aikata daga bakin aikin da ya yi a shirinsa na rage kudaden da gwamnatin jihar ke kashewa wurin biyan albasihin ma’aikata.
- Europa: An kai wa magoya bayan Man U hari a Poland
- Ina kudaden da aka kwato suke? Sarkin Musulmi ga Gwamnati
Ya sha nanata cewa gwamnaitn ba za ta ci gaba da kashe fiye da kashi 80% na kason da take samu daga Gwamnatin Tarayya ba wajen biyan albashin ma’aikata; yana mai cewa masu rike da mukaman siyasar ma matakin zai fada kansu.
A ranar Talatar gwamnatin ta sanar da sallamar masu rike da mukaman siyasa 19 ciki har da Mataimakin Shugaban Ma’aikatan gwamnan da masu ba da shawara na musamman guda biyu da sauransu.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, El-Rufai ya gode wa ’yan siyasar kan hidimar da suka yi wa jihar sannan ya yi musu fatan Allah Ya sa gaba ta fi baya kyau.
Jerin sunayen wadanda aka sallamar:
- Bala Yunusa Mohammed
- Halima Musa Nagogo
- Umar Abubakar
- Ben Kure
- Mustapha Lynda Nyusha
- Jamilu Gwarzala Dan Mutum
- Umar Haruna
- Zainab Shehu
- Stephen Hezron
- Mohammed Bello Shuaibu
- Aliyu Haruna
- Halima Idris
- Injiniya Aliyu Alhaji Salihu
- Ashiru Zuntu
- Saida Sa’ad
- Elias Yahaya
- Tasiu Suleiman Yakaii
- Samuel Hadwayah
- Ahmed Mohammed Gero.