✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Rufai ya sake rufe makarantun Kaduna

An sake rufe makarantu kwanaki kadan bayan an sake killace gwamnan jihar

Gwamnatin Kaduna ta ba da umarnin sake rufe daukacin makarantu a fadin Jihar daga ranar Laraba, 16 ga Disamba, 2020 saboda hauhawar yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 a karo na biyu.

Ma’aiatar Ilimi ta Jihar, ce umarci makarantu da su kammala duk abin da ke gabansu, a daidai lokacin da makarantu masu zaman kansu suka fara rubuta jarabawa.

“A kokarinta na hana yaduwar cutar da ceton rayuwar jama’ar jihar, Gwamnatin Kaduna na umartar dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su kammala dukkannin shirye-shiryen domin rufewa a ranar Laraba, 16 ga Nuwamnba, 2020, sabanin lokacin da aka sanar a baya.

“Wajibi ne a kammala jarabawa kafin ko a ranar Talara, 15 ga Disamba, 2020, a dukkanin cibiyoyin ilimin da ke jihar”, inji Kwamishinan ilimi, Shehu Muhammad Makarfi.

A ranar Lahadi Aminiya ta kawo rahoto inda Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce akwai yiwuwar dawo dokar hana fita a jihar, muddin aka ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar ta COVID-19.

El-Rufai wadda kamuwar wasu makusantansa ta tilasta masa sake killace kansa, ya nuna damuwa kan yadda jama’a ke watsi da matakan kariyar cutar a jihar.

Yadda makarantu za su kasance

Da yake karin haske game da rufe makarantun, Kwamishinan Ilimin jibar ya ce umarnin ya shafi makarantun gaba da sakandare.

Ya ce dalibai ba za su halarci ajujuwa ba a tsawon lokacin, amma makarantu na iya bullo da tsarin da za su bi na ci gaba da darussa gwargwadon halinsu da irin shirin da suka yi.

Game da daliban nazare, firamare da sakandare kuma, ya ce za su ci gaba da daukar darussa daga gida ta shiye-shiryen koyarwa da ake gabatarwa a gidan radiyo da talabijin na gwamnatin jihar (KSMC).

Ya kuma shawarci iyaye da su rika tabbatarwa cewa daliban sun ci gaba da karatu da daukan darusa a gida, sannan ya roki jama’a da su rika kiyaye matakan kariyan cutar domin takaita bazuwarta.

Ya ce jihar ta dauki matakin ne saboda yadda ake samun sabin masu kamuwa da COVID-19 a jihar na kama da lokacin da cutar ke ganiyarta a tsakanin watannin Afrilu zuwa Yunin 2020.