Gwamna Nasir El-Rufai ya haramta gudanar da zanga-zangar addini a Jihar Kaduna kan batun batanci da aka yi wa Annabi Muhammadu (SAW) a Jihar Sakkwato.
Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Kaduna ta fitar a ranar Asabar ta ce an dauki matakin saboda yunkurin wasu marasa kishin kasa na shirya zanga-zangar adawa da kuma goyon bayan lamarin.
- Batanci: Tambuwal ya gana da malamai kan kisan Deborah
- Batanci ga Annabi: Deborah ta wuce gona da iri —Farfesa Maqari
“An sanar da Gwamna El-Rufai halin da ake ciki kuma ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da hana duk wani nau’i na zanga-zangar addini a jihar,” a cewar sanarwar da Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya sanya wa hannu.
Lamarin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu matasa suka gudanar ce a Sakkwato, suna masu neman jami’an tsaro su saki mutanen da suka kama bisa zargin kashe matashiyar nan Deborah Samuel da suka zarga da zagin Annabi.
Arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro ta jawo an harbi mutum biyu, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC Hausa.
Rahotanni sun ce zanga-zangar ta fara ne a matsayin ta lumana kafin ta rikide zuwa jefe-jefe da duwatsu, inda su kuma jami’an tsaro suka mayar da martani da harbi da kuma hayaki mai sa hawaye.
Matasan maza da mata suna aiwatar da zanga-zangar a wurare daban-daban a fadin Sakkwato tare da kona tayoyi, da suka hada da Fadar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III.
Kazalika wasu sun yi cincirundo a kofar gidan gwamnatin jihar.
Gwamnatin Jihar ta sanar da saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 sakamakon zanga-zangar.
Sarkin Musulmi ya yi Allah wadai da kisan Deborah
Aminiya ta ruwaito cewa, Mai Alfarma Sarkin Musulmin Alhaji Muhammad Saad Abubakar ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa wata dalibar Babbar Kwalejin Ilimin Jihar Sakkwato da aka zarga da batunci ga Manzon Allah (SAW).
Wata sanarwar da fadar Sarkin ta gabatar mai dauke da sanya hannun Sakataren Masarautar kuma Danburan din Sakkwato, Saidu Muhammadu Maccido ta yi Allah wadai da kisan inda ta bukaci jami’an tsaro da su tabbatar da gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban shari’a.
Masarautar ta bukaci jama’ar Sakkwato da kasa baki daya da su ci gaba da zaman lafiya a tsakani su, yayin da jami’an tsaro ke gudanar da aikinsu.
Tuni gwamnatin Jihar Sakkwato ta sanar da rufe Kwalejin da kuma kaddamar da bincike akan lamarin kamar yadda Kwamishinan Yada Labarai Isa Bajini Galadanci ya tabbatar wa manema labarai.
Rahotanni sun ce wasu fusatattun dalibai ne suka yiwa dalibar Kwalejin da ake kira Deborah duka da kuma cinna mata wuta saboda zargin da suka mata na cin zarafin addinin Islama.
Wani daga cikin daliban Kwalejin yace Deborah tayi kalamun batancin ne a wata kafar sada zumunta da suke amfani da ita, abinda ya haifar da tashin hankalin.
Ya zuwa yanzu bayan kwanaki da faruwar lamarin, ana ci gaba da tafka mahawara a kafofin sada zumunta dangane da kisan, inda jama’a ke bayyana ra’ayoyi mabanbanta dangane da kisan.
Rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ta sanar da kama mutane 2 da ake zargin suna da hannu wajen aikata kisan.