Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya kafa kwamitin hukunta ma’aikatan Jihar da suka shiga yajin aikin da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta gudanar a kwanakin baya.
El-Rufai ya ce duk ma’aikatan da suka shiga yajin aikin za a hukunta su tare da shugabannin kungiyar kwadagon, wadanda ya ce yajin aikin da suka kira ya gurgunta harkokin jihar.
Ya ce ya riga ya kafa kwamitin bincike domin gano ma’aikatan da suka shiga yajin aikin da sai da Gwamnatin Tarayya ta sa baki, NLC ta dakatar.
A wata hira da ya yi da ’yan jarida, El-Rufai ya ce ya fara tattara bayanai daga ’yan kasuwa game da asarar da yajin aikin ya jawo musu, kuma zai tabbatar an hukunta ma’aikatan.
Sai dai kuma ya musanta sallamar ma’aikatan jihar, yana mai cewa karya NLC ta yi cewa ya sallami dubban ma’aikata.
Amma ya tabbatar cewa kananan hukumomi sun sallami ma’aikata; A kwanakin baya an kawo rahoto cewa gwamnan ya umarce su da su rage ma’aikatansu zuwa mutum 50 a kowaccensu.
A wani abu mai ama da mi’ara-koma-baya kuma, El-Rufain ya ce aikin sallamar ma’aikatan da gwamnatinsa ta shirya na ci gaba, amma zai mayar da hankali ne a kan masu amfani da takardun bogi.
Ana kuma iya tunawa cewa a lokacin yajin aikin na kwanakin baya, gwamnan ya kori daukacin ma’aikatan jinya ’yan kasa da matakin albashi na 14, ya kuma ba da umarnin a dauki sabbi.