Gwamnatin Jihar Kaduna ta nada kwamitin binciken rikicin Zango Kataf da ya yi sanadiyyar rasa rayuka 2,000 a shekarar 1992.
Hakan na dauke ne a wata takardar da Mai ba wa Gwamna Nasiru El-Rufai Shawara a kan Harkokin Jarida, Muyiwa Adekeye ya fitar.
- Kaduna ta fadada dokar kullen Zangon Kataf da Kauru
- Ana zaman dar-dar bayan an yi wa manomi yankan rago a Zangon Kataf
Bayanin da ke kunshe cikin takardar ya zayyana cewar, “Rikicin da aka yi a watan Fabrairu 1992 ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 95, yayin da 233 suka jikata.
“A rikicin watan Mayun 1992 mutuwar ta karu zuwa 1,528 a Zangon-Kataf, sai kuma sauran mutum 305 a Zariya da Ikara da wasu sassa na Jihar da aka samu barkewar rikicin”, inji shi.
“Sai dai duk da kwamitin binciken da aka gudanar a wancan lokacin, gwamnatocin baya ba su aiwatar da rahoton da aka ba su ba.
“Sakamakon faruwar irin wancan rikicin a watan Mayu ne gwanatin za ta kakkabe rahotannin da suka gabata.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Abun allawadai shi ne yadda daya daga cikin ababan da Maishari’a Cudjoe ya danganta da tushen rikicin da Zangon-Kataf a 1992 har yau shi ke haddasa kashe-kashe da sauran laifuka da ke faruwa bayan shekaru 28 da aukuwar na farko”, inji Muyiwa.