Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Fatakawal, Dokta Austen Sado, ya caccaki Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna dangane da dambarwar da ta wakana tsakaninsa da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC).
Dokta Sado ya ce Gwamna El-Rufai yana takama tare da yi wa kansa kallo a matsayin wanda ya fi kowa ilimi da wayewa a zamanance.
- Ibrahim Attahiru: Tarihin Babban Hafsan Sojan Kasa na Najeriya
- Shugaban makaranta ya sa dalibi dauko salula daga masai
A cewarsa, “Gwamna El-Rufai mutum ne da yake ganin ya fi kowa ilimi.”
Da yake tsokaci dangane da takun-sakar da ta shiga tsakanin El-Rufai da Kungiyar Kwadago, Dokta Sado ya ce duba da yadda Gwamnan ya ke takama da ilimi ya kamata a ce tunkari matsalar ta hanyar da ta dace.
Dokta Sado ya bayyana mamakinsa kan dalilin da ya sanya Gwamnan ya bayyana neman Shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa, Ayuba Wabba ruwa a jallo, lamarin da ya ce “tabbas Gwamnan ya nuna girman kai ga talakawa a yayin yajin aikin.”
“A zamanin mulkin soja na Janar Olusegun Obasanjo ne aka gabatar da El-Rufai a matsayin daya daga cikin hazikai da su ka san ya kamata, saboda haka ina tsammanin wannan dalilin ne ya sa yake jin ya fi kowa ilimi.
“Abun kunya ne a ce mutum tamkar El-Rufai yana korar ma’aikata daga aiki ba bisa ka’ida ba.
“Wannan rashin amfani da ilimi da mai ya yi kama da har El-Rufai zai umarci Jami’ar Jihar Kaduna ta gabatar da rajistar ma’aikatanta masu zuwa aiki duk rana ga Sakataren Gwamnati Jihar da kuma Kwamishinan Ilimi.
“Wannan mataki na rashin amfani da ilimi da mai ya yi kama, don ya kamata Gwamnan ya san duk wasu tanade-tanade da doka ta yi.
“Wannan shi ya nuna irin jahilcin da El-Rufai yake fama da shi kuma ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa, irin wannan mutane masu ikirarin cewa su ne manya a cikin wannan al’umma, ba su san komai ba ko kadan.
“Shin El-Rufai ya fahimci abin da ake nufi da kasancewar mutum a matsayin Shugaban Kungiyar Kwadago a Najeriya da har zai bayar da umarnin a kama Ayuba Wabba”?
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne aka sa zare tsakanin Gwamnati da Kungiyar Kwadago a Jihar Kaduna, yayin da kungiyar ta bai wa dukkanin ’ya’yanta umarnin shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar a fadin Jihar.
Kungiyar Kwadagon ta tsunduma yajin aikin ne domin gargadin Gwamnatin Jihar a wani yunkuri na neman ta sauya hukuncin sallamar dubban ma’aikata da ta yi.
Sai dai tun a ranar Alhamis aka janye yajin aiki, inda aka fara zaman sulhu tsakanin bangarorin biyu yayin da Gwamnatin Tarayya ta nemi su yayyafawa zukatansu ruwa.