✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El Clásico: Real Madrid ta hau saman teburin La Liga

Sau uku a jere ke nan Zidane na jagorantar Real Madrid ga nasara a El Clásico

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta dare saman teburin gasar La Liga na kasar Sifaniya bayan da ta lallasa Barcelona da ci 2 – 1 a wasan El Clásico da suka fafata ranar Asabar da dare.

Real Madrid ta dare kan teburin ne daga matsayi na uku, sai kuma abin da hali ya yi a wasan Atletico Madrid, wadda kafin wasan na El Clásico ita ce a saman teburin.

A halin yanzu, Madrid da ke saman teburin La Liga na da maki 66, sai Atletico Madrid da maki 66, sannan Barcelona, Barcelona da maki 65.

Wasan shi ne na 279 tsakanin manyan abokan hamayyan na kasar Sifaniya. A tsawon tarihin Clásico da ya faro tun a shekarar 1902, Barcelona ta samu nasara 115, Real Madrid 101, sannan suka yi kunnen doki sau 63.

Sai dai kuma a wasanni shida na baya-bayan nan, sau uku ke nan da Real Madrid ta doke Barcelona a El Clásico, sun yi kunnen doki a wasa daya da aka tashi babu ci, Barcelona kuma ta lashe wasanni biyu.

Mai horar da kungiyar, Zinadine Zidane, yanzu shi ne wanda ya taba cin wasannin Clásico uku a jere tun daga shekarar 1979.

Tsanllen badaken da Real Madrid ta yi a halin yanzu ya mayar da Barcelona a matsayi na uku; Ta kuma ci kwallayen nata ne tun kafin tafiya hutun rabin lokaci, ta hannun Karim Benzema (a minti 13) da Toni Kroos (a minti 28), a lokacin Barcelona ba ta da ko daya.

Karim Benzema

Kafin wasan na Asabar, an yi wasanni tara na Clásicos ba tare da Karim Benzema ba tare da ya ci kwallo ba, shi kuma Toni Kroos, wasanni 17.

Bayan dawowa hutun rabin lokaci da minti 15, Óscar Mingueza na Barcelona ya zura kwallon farko a ragar Real Madrid.

Óscar Mingueza

Kwallonsa na farko da ya taba zurawa a ragar Madrid ke nan a El Clásico; Lionel Messi ya kai hari sau tari gidan Madrid amma duk ba wanda ya ci.

Clasico na bakwai ke nan a jere da Messi ya buga tun bayan tafiiyar Cristiano Ronaldo Real daga Madrid, ba tare da ya ci kwallo ba.

Kafin yanzu, Barcelona ba ta taba lashe gasar La Ligan a kakan wasar da ta sha kashi a hannun Real Madrid ba.

An fara wasan da yi shiru na minti daya domin tunawa da Antonio Calpe na Real Madrid.

A wasannin El Clásico shida na karshe da manyan kungiyoyin biyu suka yi arangama da juna, an tashi ne kamar haka a gasar La Liga:

  1. FC Barcelona 1 – 3 Real Madrid
  2. FC Barcelona 0 – 2 Real Madrid
  3. FC Barcelona 0 – 0 Real Madrid
  4. FC Barcelona 1 – 0 Real Madrid;
  5. Sai kuma FC Barcelona 3 – 0 Real Madrid a gasar Copa Del Rey.