✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Clasico: Real Madrid da Barcelona za su barje gumi a Saudiyya

Real Madrid da Barcelona za su sake barje gumi a Kasar Saudiyya.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid da Barcelona za su kara a gasar Super Cup a kasar Saudiyya.

Wannan ita ce shekara ta biyu da kasar Saudiyya take daukar nauyin gudanar da gasar.

Kungiyoyin biyu za su barje gumi ne a ranar Laraba da misalin karfe 8 na dare.

Atletico Madrid kuma za ta kara da Athletic Bilbao a ranar Alhamis.

Kowane wasa zai kasance daga shi sai wasan karshe na Gasar ta Super Cup.

A shekarar da ta wuce Real Madrid ce ta yi nasara lashe kofin, inda ta doke Atletico Madrid a bugun fenareti.

Sai dai masu hasashe kan harkokin wasanni na ganin Real Madrid za ta iya nasara a kan Barcelona, duba da irin matsalolin da Barcelonar ke fuskanta a bana.