Dalibar nan da ake zargi da kara wa kanta maki a jarrabawar JAMB ta amince cewa da kanta da sauya sakamakon jarrabawar.
Ejikeme Mmesoma mai shekarar 19, wadda tsohuwar daliba ce a makarantar ‘Anglican Girls’ Secondary School’ a Jihar Anambra, ta bayyana yadda ta kara wa kanta maki a takardar sakamakon jarrabawar.
- Tinubu zai halarci taron ECOWAS a Guinea-Bissau
- Tinubu zai biya bashin takardun lamunin ƙasashen waje a watan Yuli
A ’yan kwanakin nan, batun ya janyo ce-ce-ku-ce, tun bayan da hukumar da ke shirya jarrabawar ta karyata makin da dalibar ta yi ikirarin samu a sakamakon.
Ita dai Hukumar JAMB ta ce dalibar ta samu maki 249, sabanin maki 362 da take ikirarin samu, to sai dai a lokacin dalibar ta kafe cewa sakamakon da take ikirari shi ne na gaskiya.
Lamarin da ya sa gwamnan Jihar Anambra Charles Soludo ya kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.
Kwamitin ya gayyaci dalibar da shugabar makarantar da kuma jami’an Hukumar JAMB domin jin bahasin kowanne bangare.
Hukumar ta JAMB ta ce sakamakon da dalibar ke ikirarin samu wanda ke dauke da maki 362 sakamako ne na bogi.
Haka kuma JAMB din ta bayyana yadda Ejikeme Mmesoma ta yi ta yunkurin neman sakamakon jarrabawar tata a shafin hukumar cikin sa’o’i da dama, kuma a duk wadannan lokuta sakamako daya take samu daga hukumar wanda ke nuna cewa ta samu maki 249.
To sai dai Ejikeme Mmesoma ta shaida wa kwamitin cewa ta amince da wannan bayani da jami’an hukumar ta JAMB suka yi wa kwamitin.
Ta bayyana cewa da kanta ta kara makin sakamakon jarrabawar tata.
Ta ce ta yi amfani da wayarta wajen sauya sakamakon jarrabawar, kafin ta fitar da takardar sakamakon jarrabawar.
Kwamitin ya yi kokarin gano dalilin dalibar na aikata wannan laifi, to sai dai ta ce ba ta da wani kwakkwaran dalili.
Daga karshe kwamitin ya bukaci dalibar ta gaggauta neman afuwa bisa wannan laifi da ta aikata, ta hanyar rubuta wasikar neman afuwa ga Hukumar JAMB da hukumar Makarantar da ta kammala, sannan zuwa ga gwamnatin Jihar Anambar.
Sannan kwamitin ya bukaci dalibar ta je a duba lafiyar kwakwalwarta, tare da yin kira da duka daliban da ke rubuta jarrabawar da su tsaya inda dokokin hukumar ya iyakance musu.
Daliba mafi samun nasara ta samu kyauta
Tuni dai dalibar da ta fi takwarorinta samun sakamako mai kyau a jarrabawar bana, Kamsiyochukwu Umeh ta samu kyautar zunzurutun kudi har Naira miliyan daga Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Erisco Foods Limited, Dokta Eric Umeofia.
Dokta Umeofia ne ya bayyana hakan yayin wata hira da jaridar Punch a ranar Juma’a.
Daliba Kamsiyochukwu Umeh ta makarantar Deeper Life High School da ke Mowe a Jihar Ogun, ta samu maki 360 daga 400 a sakamakon jarrabawar JAMB da ta zana a bana.