✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai biya bashin takardun lamunin ƙasashen waje a watan Yuli

Rahotannin baya-bayan nan na nuni da cewa, basusukan da ake bin Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 82.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa na cika alkawarin da ya dauka na biyan basussukan da ake bin kasar.

Bayanai sun ce a yanzu gwamnatin Tinubu ta shirya biyan bashin takardun lamunin ƙasashen waje (Eurobonds) na dala miliyan 500 a watan Yulin 2023.

Wannan matakin ya nuna yadda gwamnatin ta mayar da hankali kan alhakin kudi da kuma jajircewarta na ci gaba da tabbatar da amincin Najeriya a kasuwannin hada-hadar kudi ta duniya.

Ta hanyar cimma wannan gagarumin biyan basussuka, Najeriya na da burin bunkasa kwarin gwiwar masu zuba jari da kuma karfafa sunanta a matsayin amintacciyar kasa mai karba da biyan bashi a fagen kasa da kasa.

Rahotanni daga Ofishin Kula da Basussuka (DMO) na nuni da cewa, Najeriya na shirin biyan dala miliyan 500 na Eurobond a wannan watan Yulin 2023, wanda ya yi daidai da sharuddan lamunin.

Kudirin wanda aka samu shekaru biyar da suka gabata akan kudi kashi 6.375% a duk shekara, yanzu za a biya shi, domin ko dai Najeriya ta biya bashin ko kuma ta kara kudaden da ake bukata.

Yawanci, ana biyan basussukan Eurobond daga asusun ajiyar waje na kasar ko kuma ta hanyar asusu na musamman da aka kebe don biyan kudin waje.

Sai dai Najeriya ta fuskanci kalubale a wannan fanni, inda asusun ajiyarta na waje ya ragu da kusan dala biliyan uku a bana, sakamakon raguwar sayar da danyen mai.

Bugu da kari, jawo hannun jari na kasashen waje ya sami tasgaro da wahala, hakan yayi tasiri da rashin kudin.

To sai dai kuma, ba a taba samun shakku kan yadda kasar za ta iya biyan bashin ba, duk da raguwar kudaden da aka samu, sabanin sauran kasashen dake kudu da hamadar Sahara irin su Ghana, wadanda sai da suka sake yin shawarwarin lamuni bayan sun gaza.

Rahotannin baya-bayan nan na nuni da cewa, basusukan da ake bin Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 82.

Masana dai na ganin da wuya Najeriya ta nemi karin kudin Euro saboda kalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta na rancen kudaden kasashen waje.

Sai dai kuma nasarar da aka samu na biyan bashin dalar Amurka miliyan 500 na Eurobond ya sake tabbatar da aniyar Najeriya wajen tafiyar da harkokin kudi da kuma sanya kasar nan a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya.