✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta titsiye Daraktan NDDC kan zargin badakalar N25bn

Har yanzu ana ci gaba da titsiye shi

Jami’an Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) yanzu haka na ci gaba da titsiye Daraktan Kudi na Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Eno Ubi Otu.

Jami’an hukumar dai sun tsare Otu ne da misalin karfe 11:15 na safe dangane da zargin karkatar da kudaden haraji sama da Naira biliyan 25 mallakin NDDC.

Wata majiya a Hukumar ta shaida wa Aminiya cewa, har yanzu Daraktan na tare da jami’an EFCC  zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A cewar jami’an, kama Otu ya biyo bayan wani zuzzurfan bincike kan rahoton binciken kwakwaf a hukumar ta NDDC.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, amma abin ya ci tura.

Yayin da wakilin namu dai ya kira wayarsa bai amsa ba.