Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annatic (EFCC) ta ce mika wani dan Najeriya ga kasar Amurka bisa zargin shi da aikata almundahana, da amfani da haramtattun kudi.
EFCC ta bayyaan cewa laifukan Gbadesin, sun kuma hada da damfarar Dala dubu 148 ta intanet da ya yi wa wata Ba’amurkiya ta hanyar fakewa da soyayya a ranar 2 ga watan Satumbar 2021.
- Taimaka wa ’yan bindiga: An tsige sarakuna 2 da hakimi a Zamfara
- Majalisa ta kirkiri dokar da haramta biyan kudin fansa
Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwajaren ya ce sun shirya mika mutumin ne bayan takardar bukatar hakan da ofishin Atoni Janar na kasa ya mika a gare su.
Hukumar ta ce laifukan sun saba da sashi na 16 da 1349 da kuma 1958 na kundin dokar Amurkan, wanda hukuncinsa shi ne daurin shekara 20.
Uwajeran ya ce wanda ake zargin dai zai gurfana ne a gaban kotun lardin New Mexico da ke Amurkan din girbar abin da ya shuka.