Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC), ta kwato N1bn daga hannun wani ma’aikacin gwamnati da ba a bayyana sunansa ba.
Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a loakcin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan Kudaden Shigan Hukumomin Gwamnati.
- Saudiyya ta bukaci a kawo karshen zubar da jini a Gaza
- ’Yan bindiga sun harbe dan Sarkin Kontagora
- ’Yan sanda sun cafke masu satar mutane a Filato
“Akwai abubuwa da dama da muke bukatar tsohewa ba wai iya kudaden shiga ba kadai, saboda ko a makon jiya sai da muka kwato Naira biliyan daya a hannun wani ma’aikacin gwamnati,” a cewarsa.
Ya ce a makon da ya gabata ne aka gano kudin da ke ajiye a asusun bankin ma’aikacin gwamnatin.
Bawa ya ce EFCC za ta amince da rahoton kwamitin da za su gabatar da zarar sun kammala bincike kan lamarin.
“Na yi farin ciki kan yadda na ga kwamitin na gudanar da binciken.
“A wannan lokacin, kasar nan ba wai iya kudaden shiga kadai za ta toshe hanyoyin zurarewarsu ba, har hanyoyin da ake samun kudaden ya kamata a toshe su,” cewar Bawa.