✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kwace gidajen ma’aikacin Fadar Shugaban Kasa

An kwashi ’yan kallo bayan sojoji sun nemi hana sa wa gidajen jan fenti.

Hukumar Yaki da Cin Hanci ta EFCC ta kwace gidajen Janar Jafaru Mohammed, Daraktan Kudi a Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro.

Gidajen ma’aikacin Fadar Shugaban Kasar da EFCC ta kwace ta kuma sanya musu jan fenti, suna rukunin gidajen alfarma na Sun City da ke Abuja.

Hukumar ta kwace gidajen ne bisa umarnin Mai Shari’a Folashade Giwa-Ogunbanjo ta Babbar Kotun Tarayya bayan karar da EFCC din ta shigar tana neman kwace gidajen Janar din.

An kwashi ’yan kallo tsakanin sojojin da ke gadin gidan Janar din da jami’an EFCC da suka je domin sanya musu alama a safiyar Laraba.

Sojojin da ke gadin gida mai Lamba 25, Osaka Street, sun yi wa jami’an na EFCC jan ido suka kuma tabbar ba a sa wa gidan jan fentin EFCC ba.

Majiyarmu ta ce, a yayin da ake cacar baki tsakanin wasu sojoji biyu da jami’an EFCC, sai wasu sojoji kusan 20 suka isa wurin a cikin motoci, suka hana a sanya wa gidan alamar EFCC.

“Sun zo a cikin watar farar Hilux da bakar jif, sauran kuma a cikin karamar mato wasu kuma a cikin bas,” inji majiyar.

Wakilinmu ya ziyarci gidan domin gane wa idonsa, amma fusatattun sojojin da ke sintiri suka yi masa barazanar korar shi.

Wakilin namu ya ziyarci daya gidan mai lamba 52, Main Street, a rukunin gidajen na Sun City, inda ya iske EFCC ta sa masa jan fenti.

Amma bayan wasu awanni, sai aka rufe jan fentin da EFCC ta goga bangon ginin da kofar shiga gidan.