Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Najeriya EFCC, ta cafke wasu mutum 33 da ake zargi da damfara a shafukan intanet.
Sanarwar da kakakin hukumar reshen Ibadan, Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Alhamis, ta ce an cafke ababen zargin ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
- Gwamnatin Tarayya ta bai wa ma’aikata hutu ranar Litinin
- Zaben 2023 ba zai tabbata ba muddin babu tsaro a Najeriya — PDP
Kamfanin dillancin labarai na kasar NAN ya ruwaito cewa, EFCC ta kama ababen zargin ne ranar Talata a unguwar Adigbe da ke yankunan Oloke da kuma Idi Ori a garin Abeokuta.
Mista Uwujaren ya ce sun samu wannan nasara ce bayan bayanan sirri da suka samu kan zargin miyagun ayyukan da ababen zargin ke aikatawa.
Daga cikin ababen da aka samu a hannunsu a cewar Uwujaren sun hada da motoci 18, wayoyin salula, na’urorin komfuta da sauransu.
Y ace nan ba jimawa za a gurfanar da su a gaban Kuliya da zarar sun kammala binciken da suke gudanarwa a kansu.