Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ziyarci tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo a Jihar Ogun, domin tattauna al’amuran da suka shafi siyasar Najeriya.
Taron ya gudana ne a gidan Obasanjo, tare da tsohon gwamnan Jihar Kuros Ribas, Donald Duke.
- Yadda marasa lafiya ke fama saboda tsadar magani
- Ba mu nemi Jonathan don yi mana takara a 2027 ba — PDP
Kwankwaso ne, ya bayyana ziyarar a shafinsa na X.
Ya ce sun tattauna kan muhimman al’amuran suka shafi ƙasar nan, musamman makomar siyasa da shugabanci a Najeriya.
A cikin rubutunsa, ya ce: “Na yi farin ciki da ziyartar tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta, tare da abokina Donald Duke da wasu abokan aiki.
“Mun tattauna kan muhimman al’amuran ƙasa, musamman makomar siyasa da shugabanci a Najeriya. Muna godiya ga Baba saboda karamcinsa da goyon bayansa.”
Idan ba a manta ba, a watan Nuwamba Obasanjo ya halarci bikin auren ’yar Kwankwaso a Kano.
A wajen bikin, Obasanjo ya sanya jar hula, wand hakan ya nuna wata dangantawa da Kwankwasiyya.
Obasanjo ya samu tarba da girmamawa daga Kwankwaso da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Wannan ganawar da shugabannin suka yi ba za ta rasa nasaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 ba.
Ga hotunan yadda ziyarar ta kasance: