Rahotanni sun nuna cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki ta kama tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.
EFCC ta kama Sanata Hadi Sirika ne kan zargin badakalar Naira biliyan 8.06 a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wasu jami’an hukumar sun ce an kama shi ne a ci gaba da binciken da EFCC ke yi kan ma’aikatar sufurin jiragen sama a lokacin shugabancinsa.
Hadi yana fuskantar zargin almundhanar kwangila, karkatar da kudade, amfani da ofishinsu ta hanyar da ba ta dace ba da kuma safarar kudaden haram.
Bayanai sun nuna a ranar Talata EFCC ta tsare shi, bayan ya gabatar da kanta a babban ofishinta da ke Abuja domin amsa tambayoyi.
Ya je amsa tambayoyi ne kan zargin ba Engirios Nigeria Limited mallakin kaninsa mai suna Abubakar kwangilar makudan kudade.
Ya ba wa kanun nasa kwangila ne duk kuwa da cewa kanin nasa ma’aikacin gwamnati.