✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya rage farashin Dala ga ’yan canji

CBN ya kara rage farashin da zai ba ’yan canji Dala zuwa N1,021

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dawo sayar da Dala Dala kai-tsaye ga ’yan canji a kan farashi N1,021.

Sanarwar da CBN ya fitar na sanar da kamfanonin canjin kudade cewa zai rika ba su Dala a kan farashin N1,021.

Karo na biyu ke nan a wannan watan na Afrilu da CBN ya rage farashin Dala — bayan na farkon da ya sanya a kan N1,036.

“Muna sanar da ku cewa CBN zai rika ba wa kamfanonin canji Dala 10,000 a farashin N1,021 kowace Dala.

“Su kuma za su sayar wa masu bukata su dora ribar da ba ta haura kashi 1.5% ba farashin da suka samu ba.”

Daga nan babban bankin ya bukaci yan canjin da ke bukata da su tura kudadensu zuwa susun da ya bayar sannan su kai takardun shaidar biya da sauran takardun da ake bukata rassansa domin su karbi Dala.

A cewarsa, hakan na daga cikin matakan farfado da darajar Naira, ganin yadda a yan kwanakin nan ta dan yi kasa.

A watan Fabrairu CBN ya fara sayar wa kamfanonin canji $20,000 a kan N1,301/$.

Daga bisani ya rage yawan dalar da yake ba kowannensu zuwa $10,000 a kan farashin N1,251/$1.

A farkon watan nan na Afrilu kuma bankin ya karya farashin Dala zuwa N1,101/$1 da sharadin kada ribar da za su dora ya haura 1.5%.