✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama mai damfara da sunan Shugaban Kwastam

Hukumar Yaki da  yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama wani mutum mai suna Azeez Yakubu Afolayan, da ake zargi yana damfarar mutane ta…

Hukumar Yaki da  yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama wani mutum mai suna Azeez Yakubu Afolayan, da ake zargi yana damfarar mutane ta hanyar amfani da sunan Shugaban Hukumar Kwastam, Kanar Hameed Ali (mai ritaya), inda yake zambatar mutane cewa zai sama musu ayyukan yi.

Wata takardar da aka raba wa manema labarai a Talatar da ta gabata da ta fito daga ofishin Mukaddashin Kakakin Hukumar EFCC, Tony Orilade ta ce jami’an hukumar da ofishin yanki na Ilorin a Jihar Kwara sun kama Afolayan ne a ranar 20 ga Fabrairun da ya gabata, sakamakon takardar korafi da suka samu daga daya daga cikin wadanda ya damfara. Ya  ce wanda ake zargin ya fara samun matsala ce tun daga lokacin da wani ma’aikacin Kwastam, Hassan Garba Muhammad ya rubuta wa Hukumar EFCC takardar korafi yana zargin Afolayan da damfarar ’yan Najeriya da ke da sha’awar shiga aikin Kwastam. Zuwa lokacin da aka kama shi, ya yi nasarar damfarar mutane kudin da suka kai Naira miliyan daya.

Jami’in na EFCC ya ce a yayin bincike, wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa. Ya bayyana cewa Afolayan ya gaya musu cewa: “Na fara damfarar mutane tun a shekarar 2017 har zuwa lokacin da aka kama ni. Na samu nasarar damfarar mutum biyar. Nakan amshi adadin kudade daban-daban daga mutanen da zan damfara kuma idan mun gama shiryawa, sukan tura mini kudin ne a asusun ajiya na banki.”

“Nakan gaya musu cewa zan taimake su su samu aiki a Hukumar Kwastam ta Najeriya, amma dai na san cewa damfara ce kawai nake yi masu,” inji Afolayan.

Jami’in na hulda da jama’a na EFCC ya bayyana cewa sun samu wasu kayayyaki daga hannun mutumin da suke tuhuma, wadanda suka hada da takardun bukatar shiga aikin Kwastam, takardun daukar aikin Kwastam da kuma hotunan wasu daga cikin mutanen da ke soin shiga aikin Kwastam da ya amsa daga mutanen da ya damfara. Ya kara da cewa da zarar sun kammala bincike, za su gurfanar da shi gaban kotu.