Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, mai neman takarar shugaban kasa, a kotu kan zargin almundahanar Naira biliyan 2.3.
Okorocha, wanda ke wakiltar Imo ta Yamma a Majalisar Dattawa, an gurfanar da shi ne a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo, na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne a safiyar ranar Litinin.
- ’Yan acaba sun sake tayar da yamutsi a Abuja
- Za a fuskanci matsanancin zafi na kwana 3 a Arewacin Najeriya —NiMet
Tuni aka cika kotun, inda wasu da dama suka tsaya a yayin da suke jiran fara shari’ar.
Ana tuhumar tsohon gwamnan ne a kan tuhume-tuhume 17 da suka hada da yin sama da fadi da Naira biliyan 2.9 da EFCC ke masa.
An zarge shi da hada baki da wasu da suka hada da dan jam’iyyar APC da wasu kamfanoni biyar domin sata a asusun gwamnatin Imo, duk da cewa ya musanta aikata laifin.
Zargin Okorocha na zuwa ne kwanaki uku bayan da ya gaza samun beli.
Ya dai bayyana bukatar bada belinsa ne a kan cewa shi mai neman takarar shugaban kasa ne, inda ya jaddada cewa burinsa na siyasa zai salwanta matukar ba a bayar da belinsa ba.
Sai dai mai shari’a Ekwo, a wani takaitaccen hukunci da ya yanke kan neman belin Okorocha a ranar Juma’a, ya ce bai aminta ya bayar da belinsa ba.
A maimakon haka, alkalin ya umarci Okorocha da ya nemi gwamnatin tarayya ta tsaya masa.
Tun a satin da ya gabata ne EFCC ta yi dirar mikiya a gidan Rochas da ke unguwar Maitama da ke Abuja.
EFCC ta ce dole ne Okorocha ya mika kansa domin kama shi bayan gaza amsa gayyatar da suka yi masa.