Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da dan takarar Majalisar Dattawa na Kano ta Tsakiya na jam’iyyar APC, A.A Zaura a kotu.
EFCC ta gurfanar da dan takarar ne wanda cikakken sunansa shi ne Abdulsalam Abdulkarim Zaura a gaban wata Babbar Kotun Tarayya a Kano a yau Laraba 1 ga watan Maris, 2023 a bisa zargin laifuka hudu da suka danganci zamba.
- Zan yi aiki tukuru don cika alkawuran da na dauka —Tinubu
- Mutum 36 sun mutu a hadarin jirgin kasa a Girka
A daya daga cikin laifukan da aka karanta masa a kotun wadda Mai Shari’a Mohammed Nasir Yunusa ya jagoranta, an zarge shi da cewa a wani lokaci a watan Agusta na 2014, ya karbi dala dubu 200 daga wani Dokta Jamman Al- Azmi a Kano, da nufin zamba, da karyar za su yi wata harkar kasuwanci ta hadin gwiwa
Sai dai kamar yadda BBC ya ruwaito, wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, bayan lauya mai gabatar da kara, Aisha Tahar Habib ta karanta masa.
Lauyan A.A Zauran, Ishaq Mudi Dikko (SAN) ya nemi kotu ta bayar da belin wanda yake karewa, inda bayan ’yar takaddama, Alkalin Kotun, Mai Shari’a Yunusa ya amince da belin.
Yanzu dai an dage shari’ar har zuwa ranar 2 ga watan Mayu na 2023 domin fara sauraron kara.
Za a fara shari’ar ne tun daga farko bayan da Kotun Daukaka Kara ta soke saki da kuma wanke wanda ake zargin a kan laifin zamba da Alkalin Babbar Kotun Tarayya a Kano, A. L. Allagoa ya yi a baya.
Ana zargin A.A Zaura da zambatar wani dan kasar Kuwait dala miliyan 1.32 ($1,320,000), a kan cewa shi dan kasuwa ne da ke harkar gidaje a Dubai da Kuwait da kuma wasu kasashen Larabawa.