Hukumar Yaki da Karya Tattalin Arziki ta Kasa (EFCC) ta girke jami’anta domin sanya ido kan zaben fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ke gudana a Abuja.
Wakilan Aminiya sun ga jami’an na EFCC sun ga yadda jami’an hukumar suke kai-komo a wurin taron da ke gudana a Dandalin Eagles Square a birnin Abuja.
- An ceto mahaifiyar dan takarar Sanata a Kano daga hannun ’yan bindiga
- Elon Musk ya yi barazanar fasa sayen Twitter
Duk da cewa taron bai kankama ba, ana ganin hallarar jami’an hukumar a wurin taron na da nasaba da zargin hada-hadar kudade da sunan sayen daliget a lokacin tarukan zaben ’yan takara.
A ranar Talata ne dai jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya take fara gudanar da babban taronta da zaben dan takararta na kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Kawo yanzu dai ana ta kiki-kaka kan wanda jam’iyyar za ta fitar, inda gwamnonin Arewa ke son a bai wa yankin Kudanci, a yayin da wadansu daga cikin masu neman kujerar daga yankin Arewa suka ce ba za ta sabu ba.
Ya zuwa wannan lokaci dai sai sake lale jam’iyyar take yi a kan batun fitar da dan takara babu hammaya, lokacin fara gudanar da zaben kuma sai kara karatowa yake ta yi.