✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta fara yi wa mukarraban tsohuwar gwamnatin Katsina hisabi

A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gayyaci wasu jami’ai hudu da suka rike wasu…

A ranar Talatar da ta gabata ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gayyaci wasu jami’ai hudu da suka rike wasu madafun iko a tsohuwar gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Barista Ibrahim Shema domin su yi bayani a kan wani bincike da hukumar ke yi kan zargin yin sama-da-fadi da wasu kudaden jihar. 

Takardar gayyatar wadda wani jami’in hukumar Aminudeen Muhammad ya sanya wa hannu a madadin shugaban Hukumar EFCC wadda aka aike wa Sakataren Gwamnatin Jihar kuma ta fado hannun manema labarai ta ce, wadanda aka gayyata zuwa ofishin hukumar sun hada da Babban Akawun Kudi na Jihar da manyan sakatarorin Ma’aikatar Gona da Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje da kuma Babban Manajan Hukumar Gyaran Hanyoyi da Fitilun kan tituna (KASROMA).
Jami’ai uku, wato manyan sakatarorin biyu da Babban Manajan Hukumar KASROMA an bukaci su halarci ofishin hukumar a shekaranjiya Laraba da jiya Alhamis tare takardun bayanan irin kwangilolin da suka bayar da kasafin kudadensu na shekara da adadin kudin da suka karba da adadin da suka kashe daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Wadannan bayanai kuma ana nemansu daga sassan ayyukan gona da ayyuka da gidaje da kuma bangaren wasanni.
Shi kuwa Babban Akawun Kudi na Jihar tun a ranar Talatar hukumar ta bukaci ya halarci ofishinta da cikakkun takardun bayanan kudaden jihar tun daga shekarar 2011 zuwa watan Mayu bana. Har ila yau, an bukaci ya je da bayanin jimillar kudin da aka tura wa jihar daga Asusun Tarayya.
Kuma ya kai cikakkun bayanai a kan kasafin kudin da suka fito daga tarayya zuwa kananan hukumomi 34 na jihar da wadanda aka fitar wa Hukumar KASROMA da Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje da Ma’aikatar Gona da ta Wasanni, tun daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Takardar gayyatar mai shafuka biyu, Hukumar EFCC na bincike ne a kan jami’an domin tantance wasu bayanai da suka shafi kudaden gwamnatin jihar.