✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EFCC ta damke matashi kan damfarar baturiya N242m

Maashin ya amsar karbar £250,000 daga hannun matar cikin sulallan Bitcoin

Ofishin Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) na shiyyar Benin, ya damke wani matashi kan zargin damfarar wata ’yar kasar Birtaniya £450,000, kwatankwacin Naira miliyan 242.

EFCC ta ce ta cafke matashin ne bayan da ta samu wasikar korafi daga matar da lamarin ya shafa.

Hukumar ta ce, bayan da ta kama shi, matashin ya amsa ya karbi £250,000 daga hannun matar cikin sulallan Bitcoin.

Matashin ya ce, ya kashe kudin ne wajen sayen motoci da sarkokin zinari da gidaje da sauransu.

Wayoyin salula da kananan kwamfuta da layukan waya da sauran, na daga kayayyakin da aka kwace daga hannun matashin bayan da aka kama shi.

EFCC ta ce za ta gurfanar da matashin da zarar ta kammala bincikenta.