Hukumar yaki da masu karya tattalin arzikin kasa (EFCC) ta kama Abubakar Ahmad Sirika, kanin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.
EFCC ta kama Ahmad Sirika ne a ranar Lahadi, kan binciken da hukumar ke yi a kan ma’aikatar sufurin jiragen sama badakalar Naira biliyan 8 a karkashin Hadi Sirika.
Ana zargin a lokacin shugabancin Hadi ne aka ba Ahmad kwangila, duk da kasancewar ma’aikacin gwamnati a mataimakin darakta a mataki na 16.
A lokacin shugabancin Hadi Sirika an zarge shi da hada baki, badakala, karkatar da kudaden jama’a, kara farashin kwangila, da kuma karkatar da kudaden da suka kai N8,069,176,864.
- Kotu ta umarci gwamnati ta kayyade farashin kayan masarufi
- Za mu aurar da amarya mu sayar da ’yan daukar ta 62 —’Yan bindiga
EFCC ta bayyana cewa kudin da ake bincike a kansu, na kwangilar jiragen sama guda hudu ne da tsohon ministan ya ba wa kamfani mallakin kanin nasa mai suna Engirios Nigeria Limited.
Hukumar ta kara da shugaban kamfanin, Abubakar shi kadai ne ke sanya hannu kan asusun ajiyar kamfanin guda biyu.