✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci gwamnati ta kayyade farashin kayan masarufi

Kotun ta ba wa gwamnati wa'adin kwana bakwai ta tabbatar ta kayyade farashin kayan masarufi da na man fetur

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta umarci Gwamnatin Tarayya da kayyade farashin kayan masarufi da na man fetur cikin kwanaki bakwai.

Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa ya ba da wannan umarni ne ranar Laraba a shari’ar da mai rajin kare hakkin bil’adama Femi Falana ya maka Jukumar Kula da Farashin Kayayyaki da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kan tsadar rayuwa a kasar.

Alkalin ya ba wa gwamnati kwana bakwai ta kayyade farashin madara, fulawa, gishiri, sukari, kekuna, ashana, babura da motoci da kayayyakinsu da kuma man man fetur da dizal da kananzir.

Falana ya garzaya kotun ne yana neman ta umarci hukumar kayyade farashi ta gudanar da aikinta, kamar yada dokar dokar kayyade farashin kaya ta tanadar.

Da yake mayar da martani, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Kamarudeen Ogundele, ya ce, “Da zarar mun samu kwafin hukuncin, za mu yi nazari a kai.

“Za mu dauki matakin da zai dace da kasar kuma mana tabbatar muku cewa wannan gwamnati za ta kasance da muradin talakawa a koyaushe,” in ji shi.