A watannin baya ne aka rufe babbar Kasuwar Zage da ke garin Lalaipido (Leggal) a Karamar Hukumar Shongom a Jihar Gombe kan zargin da Fulani suka yi na kisan ’yan uwansu da suka yi wa ’yan kabilar Tangalun yankin.
Kasuwar Lalaipido da ke a duk ranar Talata babbar kasuwa da ake zuwa ci har daga kasashen waje.
A baya an rufe kasuwar ce bayan Fulanin sun raba goron gayyata ga ’yan uwansu a jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Yobe da Taraba da Filato da Gombe a shirinsu na daukar fansa kan kisan da suke zargin ’yan Tangalu sun yi wa Fulanin.
Bayan cimma jarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Fulanin da kabilun yankin wanda Sarkin Kaltungo Saleh Muhammad ya jagoranta a fadarsa, bangarorin suka amince tare da yafe wa juna da cewa komai ya wuce.
- An sace dagaci da matarsa da ’ya’yansu 5 a Kaduna
- An gano gawar Palasdinawa 210 da Isra’ila ta kashe a asibitin Gaza
Da yake jawabi, Sarkin Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad, ya bayyana farin cikinsa kan yadda sarakunan Fulanin suka amsa gayyatarsa domin tattaunawar sulhun.
Mai Kaltungo, ya shaida musu cewa Kaltungo gari ne da kowa yake da ’yancin zama ba tare da an nuna musu wani bambanci ba
A jawabansu, shugabannin kungiyar Fulanin sun nuna jin dadinsu da gamsuwa bisa yadda ake kula da ’yan uwansu a Masarautar, wanda hakan ya tabbatar musu da cewa an dauke su a matsayin ’yan uwa.
Sun kuma bayyana cewa sun yafe komai ya wuce sannan sun damka amanar duk wani Bafulatani da ke yankin Karamar hukumar Kaltungo da Shongom a hannunsa yaci gaba da rike su amana kamar yadda ya saba.