✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace dagaci da matarsa da ’ya’yansu 5 a Kaduna

’Yan bindiga su sace Dagacin Kauyen Bishini da ke Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, Samuel Danbayi, da matarsa da ’ya’yansa biyar. Aminiya ta gano…

’Yan bindiga su sace Dagacin Kauyen Bishini da ke Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, Samuel Danbayi, da matarsa da ’ya’yansa biyar.

Aminiya ta gano cewa an sace Dagacin Bishini da matarsa da ’ya’yan nasa ne a fadarsa cin daren Juma’a.

Wani mazaunin garin Ishaya Musa ya ce ’ya bindigar sun kutsa gidan dagacin ne a daren ranar Juma’a da misalin karfe 12 na dare.

Wani bafade da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa daya daga cikin matan sarkin da biyu daga cikin yaran sun tsere daga hannun wadanda suka sace su a ranar Asabar.

Ya ce, har yanzu ’yan bindigar ba su yi magana da iyalan sarkin ba.

Wani shugaban al’umma da ke Azzara, kauyen da ke makwabtaka da Bishini, ya bayyana cewa wasu mutane tara da aka sace makonni uku da suka wuce sun biya kudin fansa Naira miliyan shida

Ya ce, ’yan uwan waɗanda aka kama sun bai wa ’yan ta’addar kayan abinci da na amfanin yau da kullum kafin a sako su a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Mun nemi jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, SP Hassan Mansur, amma bai dauki waya ba, kuma bai amsa sakon tes da wakilinmu  ya aika masa domin jin halin da ake ciki dangane da lamarin.

An sace Dagacin Bishini da matarsa da ‘ya’yansa a fadarsa cin daren Juma’a.