Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta cafke Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ogun, Olakunle Oluomo.
EFCC ta kama shi ne da sanyin safiyar Alhamis a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 49 a dajin Sambisa
- Tsare Musulmi ’yan Uighur da China ke yi babban laifi ne —MDD
An dai kama shi ne bisa zargin badakalar wasu kudade, bayan jami’an hukumar sun sami bayanan sirri a kan yunkurin tafiyarsa.
Wata majiya ta shaida mana cewa yanzu haka Kakakin na can yana fuskantar titsiye a hannun jami’an hukumar.
Majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta kuma ce dama sunansa ya jima a jerin sunayen wadanda hukumar ke nema ruwa a jallo bayan ya ki amsa gayyatar da ta yi masa a baya.
An dai zarginsa tare da wasu mutane da satar sa-hannu domin karkatar da kudaden majalisar.
Sai dai da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin EFCC a ofishinta na shiyya da ke Legas, Ayo Oyewole, hakarsa ta gaza cim ma ruwa, saboda ya ki amsa kiran wayarsa.