Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta cafke wani shugaban coci kan damfarar mabiyansa kudi Naira biliyan 1.39.
Jami’an EFCC sun cafke Apostle Theophilus Oloche Ebonyi ne bayan da ya damfari mabiyansa ta hanyar sa kowannensu ya biya Naira miliyan 1.8 da cewa za su samu tallafi daga gidauniyar Ford Foundation.
Asirin Apostle Theophilus Oloche Ebonyi wanda shi ne babban limamin cocin The Rock Ministry International, ya tonu ne, bayan gidauniyar Fors ta nesanta kansa da cocinsa da ma shirin tallafin da yake ikirari.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce akasarin wadanda shugaban cocin ya damfara kungiyoyi masu zaman kansu ne da kuma daidaikun mutane a Najeriya, wadanda ya yi wa tayin shirin tallafin ta hannun gidauniyarsa mai suna Theobarth Global Foundation.
Jami’in ya bayyana cewa Apostle Ebonyi ya yi musu romon baka ne da cewa Ford Foundation za ta ba da tallafin Dala biliyan 20, domin tallafa wa masu karamin ƙarfi a cikin al’umma.
“Da haka ne ya yaudare su suka biya kudin fom da na rajista Naira miliyan 1.8 a karkashin tsarin da ya yi, har ya tara Naira biliyan 1.391 daga hannun daidaikun mutane da kungiyoyi masu zaman kansu a fadin Najeriya.
“Binciken EFCC ya gano babu wani tsari ko shiri da Ford Foundation ya yi ko wata alaƙa tsakanin su da Apostle Ebonyi.
“Hasali ma Ford Foundation ta nesanta kanta ta kowace fuska daga shi da kuma gidauniyar tasa.
“Hukumar ta kuma gano wasu kadarori biyar da aka saya da kuɗin damfarar.
“Ta kuna gano cewa har yanzu Apostle Ebonyi yana tuntubar mutane ta soshiyal midiya yana neman su shiga badaƙalar da ya kirkira da sunan Ford Foundation,” in ji kakakin na EFCC.