Jam’iyyun APC da PDP a jihar Edo na ci gaba da nuna yatsa da kuma zargin juna bayan taho-mu-gamar da magoya bayansu suka yi a fadar Oba na Benin, Oba Ewuare na Biyu ranar Asabar.
Yayin da PDP ke zargin APC da shuwagabanninta da tayar da tarzomar, ita kuwa APC tana zargin Gwamna Obaseki da jam’iyyarsa ta PDP ne.
Da yake jawabi ga ‘yan jarida a birnin Benin ranar Asabar, shugaban kwamitin yakin neman zabe na jam’iyyar PDP a jihar, Cif Dan Orbih, ya zargi APC da kokarin ganin bayan shugabannin jam’iyyarsu.
Orbih ya bayyana harin a matsayin wani yunkuri na jefa tsoro a zukatan magoya bayan Obaseki don kada su fito su zabe shi.
“Babu wata sanarwa a hukumance da ta nuna APC za ta gudanar da gangami a wurin da kuma lokacin da arangamar ta auku.
“Jim kadan da barin gwamna wajen sai wasu mutane suka far wa duk masu sanye da hulunan PDP da hari”, in ji Orbih.
‘Babu gudu…’
Ya kuma sha alwashin cewa babu wata barazana da za ta hana al’ummar jihar sake zaben Obaseki a karo na biyu.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su kama duk wadanda ke da hannu a harin da wadanda suka dauki nauyinsu.
Ita kuwa a nata bangaren, jam’iyyar APC ta bakin mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zabe bangaren yada labarai, Patrick Obahiagbon, ta ce ba hannun jam’iyyarsu a hari.
Hasali ma ya yi ikirarin cewa magoya bayan gwamnan ne suka far wa masu zanga-zangar ba-ma-yi gare shi a fadar Oba na Benin.
Ya ce bayan lamarin, an yi ta kai hari tare da cin zarafin duk magoya baya da masu sanye da rigar dan takarar PDP, Osagie Ize-Iyamu a birnin Benin.
Harbin bindiga
Obahiagbon ya kuma yi ikirarin cewa yanzu haka magoya bayan nasu na can suna samin kulawa a asibiti saboda raunukan da suka yi sanadiyyar harbin bindiga.
“Muna da labarin cewa an tattara sunayen shuwagabannin APC da aka tsara cin zarafinsu ranar zabe a jihar, ciki har da kama tsohon shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole a jajiberin zaben”, inji shi.
Idan dai za a iya tunawa, ranar Asabar din da ta gabata ne magoya bayan jam’iyyun suka yi arangama a fadar, lokacin da gwamna Obaseki da wata tawagar APC suka kai wa Oba na Benin ziyara don neman tabarruki.