✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Edo 2020: Oshiomhole ya roki gafara

Ya ce barin shugabancin jamiyyar APC zai ba shi damar gyara kuskurensa

Tsohon Gwamnan Jihar Edo kuma Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, ya nemi gafarar mutanen jihar saboda goyon bayan Gwamna Gwodwin Obaseki da ya yi a zaben 2016.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga magoya bayan jam’iyyar APC a gundumar Oredo Ward 2, da ke GRA, garin Benin, inda ya ce ya mara wa Obaseki baya ne a lokacin don ya ci gaba ayyukan da ya fara.

Amma “Na yi kuskure kwarai. Allah Ne kadai ba Ya kuskure. Yau Shekara ta 68 a duniya. Na zo na baku hakurin kuskuren da na yi na goyon bayan Obaseki.

“Na zo Edo ne in gyara kuskurena. Allah Ya bar wa Kansa sanin abun da ya faru da Ize-Iyamu a 2016. Barin shugabancin jamiyyar APC da na yi zai ba ni damar gyara kuskurena.

“Yarjejeniya ta sa Obaseki ya zama gwamna, amma Fasto Osagie Ize-Iyamu mutumin Allah ne da zai tabbatar da shugabanci na gari a Jihar Edo daga ranar 12 ga watan Nuwamban wannan shekara”, inji Oshiomhole.

Ya kuma yi kira ga dan takarar na APC da ya rike amana tare da cika alkawarin da ya yi wa jama’a.

Da yake bayani, Ize-Iyamu ya ce Obaseki bai yi wa mutanen Edo ayyuka ba saboda haka su ba shi kuri’unsu a zaben mai zuwa domin kawo canji.

Idan ba a manta ba, Ize-Iyamu shi ne dan takarar jamiyyar PDP a zaben 2016 da ya kawo Obaseki a matsayin gwamnan Edo mai ci.