✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Eden Hazard na son komawa Chelsea

Hazard ya buga wa Real Madrid wasanni 43 inda ya zura kwallaye biyar kacal.

Rahotanni daga kasar Spain na nuni da cewa, Eden Hazard ya fara tunanin barin Real Madrid inda yake neman komawa tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea.

Bayan shafe shekaru biyu a kungiyar, Hazard ya sha fama da raunuka daban-daban wanda suka kawo masa cikas na yi wa Real Madrid wani katabus.

A yayin gabatar da rahotanni, wani shahararren dan jarida na gidan talabijin na El Chiringuito da ke Sfaniya, Edu Aguirre, ya ce tuni Hazard ya fara tunanin sauya sheka duba da yadda hankalin Madrid ya karkata wajen dauko dan wasan PSG, Kylian Mbappe.

A cewarsa, da zarar Mbappe ya zo Real Madrid, ba lallai Hazard yake samun damar doka wasanni yadda ya kamata, wanda hakan na iya kawo masa koma baya a kungiyar da zai sa tauraruwarsa ta disashe.

A shekarar 2019 ce Real Madrid ta fitar da $100 wajen siyo Hazard daga Chelsea.

Dan wasan ya buga wasanni 43 a Real Madrid inda ya zura kwallaye biyar kacal.