Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), ta ba da tallafin hatsi metric ton 3,999 ga masu karamin karfi a Najeriya.
Kwamishinan ECOWAS Mista Sékou Sangaré ya bayyana hakan lokacin da ya damka kayan ga Ministan Agaji da Walwalar Al’umma, Sa’adiya Umar Faruq.
Ya ce kyautar hatsin da suka bayar kari ne a taimakawan da kungiyar ta bayar a Najeriya daga lokacin billar annobar COVID-19 ranar 27 ga watan Fabrairun 2020, zuwa yanzu.
Sangaré ya ce, kungiyar ta ba da daukin ne bayan tantance wuraren da ke da matsala da matukar bukatar, inda suka gano fiye da mutum miliyan 7,087,102 da suke fama da yunwa a Najeriya, musamman wadanda ke sansanin gudun hijira da yara masu tamowa.
Ya kuma ce akwai wasu kungiyoyin agaji da suka yi hadaka da su wajen kawo daukin a Najeriya da sauran kasashen Afirka.
A bayaninta na godiya, Ministar ta yi godiya da daukin da ECOWAS din ta kawo, inda ta ce taimakon ya zo a lokacin da zai yi wa wadanda annobar COVID-19 ta shafi tattalin arzikinsu amfani.