✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS na yi wa shirin sulhu kafar ungulu — Firaiministan Nijar

Wakilan ECOWAS sun kauracewa zaman sulhu da gwamnatin mulkin soji ta Nijar.

Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta zargi kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS da yi wa shirin sulhu da ita kafar ungulu.

Hukumomin sun yi zargin ne bisa la’akari da watsa musu kasa a ido da suka ce kungiyar ECOWAS ta yi duba da yadda ta kaurace wa zaman da ya kamata bangarorin su gudanar a yau 25 ga watan Janairun 2024 a birnin Yamai.

A tattaunawarsa da manema labarai cikin mintoci kalilan, Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine ya fara ne da zayyana yadda aka saka ranakun zama a na dagewa har sau biyu, kafin daga bisani hukumomin mulkin sojan na Nijar da shugabanin kungiyar ECOWAS su ka cimma daidaito kan ranar 25 ga watan Janairun 2025 a matsayin wacce za a fuskanci juna.

Sai dai an shafe tsawon wannan rana amma tawagar jami’an kungiyar ba ta shigo ba in ban da Ministan Harakokin Wajen Togo, Robert Dussey, da ya sauka birnin Yamai inji Fira Minista Zeine.

Sai dai yunkurin jin ta bakin Ministan Harkokin Wajen Togo Robert Dussey wanda ya halarci taron maneman labaran da Firai Minista Lamine Zeinab ya kira ya ci tura.

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar ta Nijar ya bayyana wa manema labarai cewa bai zama dole ba ministan na Togo ya yi magana.

Rashin samun izinin sauka a filin jirgin saman Diori Hamani ita ce hujjar da Lamine Zeine ya ce kungiyar CEDEAO ta sanar a matsayin abin da ya hana jami’anta halartar wannan zama.

Da ma dai tun a jajibirin wannan zama wasu kungiyoyin kawancen Kungiyoyin Front Patriotique masu goyon bayan Majalisar CNSP suka tare a wurare akalla 3 a birnin Yamai da ke kan titi mai zuwa fadar shugaban kasa daga filin jirgi da nufin bayyana wa tawagar da ECOWAS za ta turo cewa ’yan kasa ke da maganar kayyade wa’adin mulkin rikon kwarya.