Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ba za ta lamunci juyin mulki a Jamhuriyar Nijar ba.
Rahotanni sun bayyana a safiyar Laraba cewa an rufe Fadar Shugaban Kasar Nijar kan fargabar yunkurin juyin mulki.
- Sojoji sun hana shiga da fita a fadar Shugaban Kasar Nijar
- An cafke uba zai yi tsafin kudi da dan autansa
Sai dai a nasa martanin, Tinubu wanda shi ne Shugaban ECOWAS, ya ce kungiyar ba za ta amince sojoji su karbi kasar ba.
Ya ce, “Bayanin da aka samu daga Jamhuriyar Nijar na nuni da wasu abubuwa marasa dadi a kan manyan shugabannin siyasar kasar na kokarin faruwa.
“Ya kamata duk wadanda suke da hannu a Jamhuriyar Nijar su san cewa shugabannin ECOWAS da duk masu kaunar Dimokuradiyya a duniya ba za su amince da duk wani yanayi da zai kawo cikas ga Dimokuradiyya ba.
“Shugabannin ECOWAS ba za su amince da duk wani mataki da zai kawo cikas ga gudanar da halastacciyar gwamnati a Nijar ko wani yanki na yammacin Afirka ba.
“Ina so a sa ido sosai kan al’amura da abubuwan da ke faruwa a Nijar kuma za mu yi duk abin da ya dace don tabbatar da cewa dimokuradiyya ta kafu.
“Ina tattaunawa da sauran shugabanni a yankinmu, kuma za mu kare dimokuradiyyar da muke burin kafawa bisa ka’idar tsarin mulki wanda kowa ya yarda da shi.
“A matsayina na shugaban ECOWAS, na bayyana cewa Najeriya na goyon bayan zababbiyar gwamnati a Nijar, kuma ba za mu ja da baya sai mun tabbatar da dimokuradiyya.”