Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi ya ce Jiharsa ba za ta taba zama a karkarshin ikon ’yan awaren Biyafara ta IPOB ba kuma ba ruwanta da fafutukarsu.
Ya ce dokar nan ta wajabata zaman gida da kungiyar ta kafa a yankin Kudu maso gabas don nuna goyon baya ga shugabanta Nnamdi Kanu shirme ce tsantsa kuma aikin banza, don kuwa ba da Jiharsa za a yi wannan ba.
- IPOB ta sha alwashin ci gaba da kashe ’yan majalisar Anambra
- Muna roka wa Najeriya shugaba kamar Buhari a 2023 —Umahi
IPOB dai kungiya ce ta masu rajin ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biyafara karkashin jagorancin Nnamdi Kanu wanda hukuma ke tsare da shi.
Tuni dai Gwamnatin Tarayya ta ayyana kungiyar a matsayin ta ’yan ta’adda saboda ayyukanta.
Da yake zantawa da tawagar eiditoci kan karuwar matsalolin da IPOB ke haddasawa a yankin nasu, Gwamna Umahi ya fada wa ’yan kabilar Ibo cewa, “Wannan doka ta wajabta zaman gida aikin banza ce wadda ba ta da wani amfani.
“Kuma ko da ta kama a kafa kasar Biyafara, Ebonyi ba za ta taba zama daga cikinta ba.
“Na sha fada kuma zan ci gaba da fada cewa, a baya an yi amfani da mu tamkar ’yan aikin gida amma da samuwar Jihar Ebonyi mun samu ’yancin kai, sannan wani ya zo yana yi mana batun Biafra,” inji Umahi.
Gwamnan ya kara da cewa, “Kafin wannan lokaci ba mu da wani kwarin gwiwa, amma a yau mun kama hanyar sauya labarin. Sam, ba za ka ji dadi ba idan wanda ka rika a matsayin dan aiki ya fito takara.
“Don haka mu ba ’yan Biyafara ba ne, mu ma su son hadin kan Najeriya ne. Kuma ba zan daina fada cewa babu alheri a cikin dokar nan ta zaman gida-dole, kashe-kashen juna da muke yi ba daidai ba ne,” inji shi.
Kazalika, Umahi ya ce ya ji dadin ganin karshen sabanin da ake samu da mutanen sauran shiyyoyi, yana mai cewa a yanzu sun samu zaman lafiya da juna.
Don haka ya ce “Ban goyi bayan wannan dokar ba ko kadan. Kuma ina kiran jama’a kowa ya fito cikin gaskiya da tsoron Allah mu hada kai don ciyar da yankinmu gaba.”
Game da abin da ya sa Gwamnoni biyar na yankin Kudu maso Gabas ke fuskantar cikas wajen yin aiki tare, musamman game da abin da ya shafi tsaron shiyyar, Umahi ya ce “Kowace Jiha na da dokokinta, mu a jiharmu muna ganin alfanun dokinmu amma ba zan iya cewa komai game da sauran jihohin ba.”