✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ebola: CAF ta karyata batun dage wa Guinea takunkumi

Hukumar shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) ta karyata ikirarin da Hukumar kula da kwallon kafa ta Guinea (FA) ta yi na cewa hukumar ta…

Hukumar shirya kwallon kafa a Afirka (CAF) ta karyata ikirarin da Hukumar kula da kwallon kafa ta Guinea (FA) ta yi na cewa hukumar ta dage takunkumin da ta sanya mata na daina buga gasar neman zuwa cin kofin Afirka a kasar saboda cutar Ebola.
CAF ta ce har yanzu dokar tana nan daram ba ta dauki mataki a kai ba har sai bayan Kwamitin da ke lura da batun da ke karkashin hukumar ya zauna a gobe Juma’a da jibi Asabar&nbsp a Habasha kafin a cimma matsaya a game da batun.
A watan jiya ne dai Hukumar CAF ta dakatar da wasu daga cikin kasashen da suka fito daga yankin Afirka ta Yamma da suka hada da Guinea da Sierra Leone da kuma Liberiya daga yin wasanninsu a gida a gasar neman gurbin zuwa cin kofin Afirka saboda matsalar cutar Ebola da ta yi katutu a kasashen.
Hukumar ta bayyana matsayinta ne a ranar Talatar da ta wuce kuma ta ce za ta hada kai ne da Hukumar kula da lafiya ta Majalisar dinkin Duniya (WHO) kafin ta zartar da hukunci a game da wadannan kasashe.
A halin yanzu Sierra-Leone tana gudanar da wasanninta na gida ne a kasar Kongo.