✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dutse mai aman wuta ya tashi mazauna gari

Aman wutar karshe da Dutsen Nyiragongo ya yi a 2002 ya kashe mutum 250.

Aman wuta daga wani dutse da ya dangana da filin jiragen sama a Goma, gari mafi girma a gabashin Jamhuriyar Dimokoradiyya Congo, ya tilasta mazauna kaurace wa matsugunansu.

Tuni dai gwamnati ta umarci jama’a da su kaurace wa wajen yayin da dutsen ya fara aman wutar a ranar Lahadi.

A yayin da tartsatsin wuta daga Dutsen da ake kira Nyiragongo ya mamaye samaniyar birnin mai mazauna kimanin miliyan biyu, dubban mazauna Goman dauke da katifu da sauran kayayyaki sun tsere daga garin a kan sayyadarsu – inda dama suka nosa kan iyakar kasar da Rwanda.

Aman wutar karshe da Dutsen Nyiragongo ya yi a 2002 ya kashe mutum 250 inda kuma wadansu dubu 120 suka rasa muhalli.

Yana daga cikin tsaunukan da suka fi aman wuta kuma mafi hadari a duniya.

Ma’aikatar Agajin Gaggawa ta Rwanda ta ce fiye da ’yan Congo 3,500 suka tsallaka kan iyaka.

Kafar Labaran Gwamnatin Kasar ta ce za a tsugunar da masu hijirar a makarantu da wuraren ibada.

An shaida yadda sababbin huji ko ramuka suke bayyana kan dutsen, wanda hakan ya sanya aman wutar ke danaganawa zuwa cikin birnin bayan da a farko yake nosar gabashi ta yankin Rwanda, inji Dario Tedesco, masanin aman wutar dutse da ke zama a Goma.

“Yanzu garin Goma ne aman wutar ta nufa,” inji Tedesco.

“Kuma wannan ya yi kama da aman wutar 2002 ina ganin aman wutar ya dumfari tsakiyar birnin.

“Watakila ya tsaya kafin can din ko kuma ya ci gaba. Yana da wahala a iya hasashen mai zai faru,” inji shi.

Celestin Kasereka, jagoran masana kimiyyar da ke bincike a Cibiyar Nazarin Aman Wutar  Goma, OVG, ya fada wa manema labarai cewa ba ya tunanin aman wutar dutsen zai dangana da cikin garin Goman.

Wata majiyar Majalisar Dinkin Duniya ta ce an dauke dukkanin jiragen saman majalisar zuwa birnin Bukavu da ke kudanci da kuma Entebbe mai makwabtaka da Uganda.

Rahotanni sun bayyana cewa, an dauke wuta a galibin unguwannin garin na Goma.

Firai Minista Jean-Michel Sama Lukonde ya kira taron gaggawa a Kinshasa babban birnin kasar, inda gwamnati ta kaddamar da shirin kwashe al’umma daga Goma.

“Muna fatan matakan da muka dauka a yammacin Asabar za su bai wa jama’a damar kai wa tudun mun-tsira,” inji kakakin gwamnatin kasar, Patrick Muyaya.

Shugaba Felix Tshisekedi zai katse bulaguron da yake yi a nahiyar Turai domin komewa kasar a ranar Lahadi, kamar yadda fadar Shugaban ta wallafa a Tiwita.

Fargaba na yaduwa cikin hanzari a Goma

“Muna cikin zullumi sakamakon kwatsam muka hasken da ba na lantarki ba ya turnuke gaba daya samaniyar birnin,” inji John Kilosho.

“Ba mu ma san me za mu yi ba. Kai ba wanda ya san ko tunanin da ya kamata mu yi ba. Babu bayanai.”

Sauran wadanda suka tsere daga kwaryar birnin da kauyuka da ma makwabtan yankunan da ke kewaye wadanda suke fuskantar barazanar aman wutar daga barayin arewacin wajen birnin sun nuna yadda hantarsu ta kada.

“Mun kalli samaniya sai kawai mu ka ga ta koma ja zur – kalan aman wutar ke nan,” inji Richard Hazika Diouf daga yankin Majengo mai makwabtaka.

Masu sa ido kan dutse mai aman wuta sun damu da aman wutar da ta faru shekara biyar da suka wuce a tsaunin Nyiragongo, wanda ya yi kama da irin wanda ya auku a 1977 da 2002.

Kwararru a cibiyar ta OVG, mai bincike kan aman wutar dutsen Goma, da ke sa ido kan tsaunin na Nyiragongo, suna fama wajen gudanar da binciken da ya kamata tun bayan da Bankin Duniya ya janye tallafin kudin da yake bayar wa saboda zarge-zargen almundahana.