Gwamnatin jihar Kano ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 don tallafawa waɗanda ibtila’in gobara ta shafa a Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a jihar Jigawa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da bayar da tallafin ne a wata ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi Danmodi a gidan gwamnati da ke Dutse ranar Alhamis.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa an bayar da tallafin ne domin a kai ɗauki ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma tallafa wa waɗanda suka jikkata a gobarar.
Ya bayyana ƙaƙƙarfar alaƙar tarihi da al’adu a tsakanin jihohin Kano da Jigawa, inda ya jaddada haɗin kan Kano da maƙwabtanta a wannan lokaci na jimamin ibtila’in.
Gwamnan ya kuma jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da kuma waɗanda suka samu raunuka, inda ya yi addu’ar Allah Ya kiyaye afkuwar irin wannan a nan gaba.
A nasa martanin, Gwamna Umar Namadi ya bayyana matuƙar godiya a madadin al’ummar jihar Jigawa, inda ya gode wa jihar Kano bisa irin gudunmawar da ta bayar a wannan mawuyacin lokaci.
Ya ba da tabbacin cewa, za a yi amfani da kuɗaɗen cikin adalci wajen taimakon waɗanda abin ya shafa da iyalansu.
Gwamna Namadi ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yammacin ranar Alhamis mutane 167 ne suka rasa rayukansu, kuma mutane 67 ke karɓar magani a cibiyoyin lafiya daban-daban a ciki da wajen jihar.