Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa laifi ne abin da jami’anta ke yi na cin zarafi da cin zalin fararen hula saboda sun sanya kayan soja ba bisa ƙa’ida ba.
Shugaban Sashen Hulɗar Sojoji da Fararen Hula na rundunar, Manjo-Janar Gold Chibuisi, bayyana cewa rundunar tana hukunta duk jami’inta da aka kama da laifin cin zalin farar hula saboda sanya kayan sojoji.
Ya ce duk da haka doka ta haramta wa fararen hula sanya kayan sojoji ba bisa ka’ida ba, kuma laifi ne da zai iya kai su gidan yarin.
Manjo-Janar Gold Chibuisi, ya ci gaba da cewa doka ba ta ba ta ba sojoji ikon hukuntawa balantana cin zalin masu aikata hakan ba. Sai kuma ta ba su ikon kama masu sojan gona da kayansu, kuma an ba sojoji horo a kan kama masu aikata hakam, su miƙa shi ga ’yan sanda domin gurfanarwa a gaban ƙuliya.
- Aminu Bayero ya naɗa Sanusi a matsayin Galadiman Kano
- NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”
“Duk waɗannan abubuwan — na cin zalin da cin zarafin da sojoji ke yi wa masa sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba — ba daidai ba ne. Muna kuma wayar da kansu a game da hakan, sa’annan duk sojan muka samu hujja a kansa kuma, muka yi masa hukunci mai tsanani,” in ji shi.
‘Sanya kaya soja haramcin ne ga fararen hula’
Sai dai kuma Manjo-Janar Gold Chibuisi ya yi gargadi ’yan Najeriya su guji sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa mutunta kayan sojo wani muhimmin sashi ne na ƙarfafa tsaron ƙasa.
Ya jaddada cewa yin amfani da kayan aikin soja ba bisa ƙa’ida ba ga mutanen da ba su da izini ya saɓa wa doka kuma yana taimakawa ayyukan laifi, yana mai cewa bin irin wannan shawarar zai samar da yarda tsakanin sojoji da jama’a.
Ya yi wannan gargaɗin ne a Abuja a ƙarshen mako a wani taron tattaunawa da ’yan jarida, inda ya ce, “Sanya kayan sojoji ga mutumin da ba soja ba ya saɓa wa dokar ƙasa. Idan kai ba soja ba ne ko jami’in tsaro, yin amfani da unifom ɗinsu — ko kana son sa ko ba ka so — laifi ne.”
Chibuisi ya jaddada cewa dole ne a mutunta doka don kiyaye mutunci da tsaron rundunonin soji, yana mai gargadin cewa masu aikata laifin na iya fuskantar ɗauri a kurkuku.
“Idan kuna son aikin soja, ku shiga aikin soja. Kada ku saka kayanmu idan ba a cikinmu kuke ba,” in ji shi.
Game da haɗarin tsaro da ake tattare da sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba, Chibuisi ya bayyana cewa masu aikata laifuka na ƙara amfani da kakin soja don aikata laifuka, wanda ya sa ya zama da wahala ga fararen hula da hukumomin tsaro su gane sojojin gaske da na bogi.
Ya ce, “A halin yanzu, akwai ’yan fashi da yawa da ke amfani da kayan soji don aikata laifuka. Idan mutane suka ci gaba da yin ado da kayan sojoji, ta yaya za ku bambance tsakanin ɗan fashi da sojan gaske?”
Ya yi kira ga iyalai da al’ummomi da su taimaka wajen wayar da kan jama’a daga matakin gida.
“Idan wani da kuka sani ba ne ya fito sanye da ku ce masa, ‘Dakata, yau ka shiga aikin soja, cire wannan abin mana.’ Ka guji a kama ba.”
Janar din ya ci gaba da bayanin cewa an horar da sojoji don kama fararen hula da aka samu sanye da kayan soja kuma a miƙa su ga ’yan sanda don gurfanar da su a gaban kotu.
Ya kuma jaddada mahimmancin hana aikata laifin kafin ya faru: “Wani gefen shi ne sojojinmu su yi abin da ya dace idan sun ga haka, ɗayan gefen kuma shi ne fararen hula kada su yi hakan kwata-kwata.”
Yayin da yake bayyana bambanci tsakanin Najeriya da sauran ƙasashe a kan wanna batu, Manjo-Janar Chibuisi ya ƙara da cewa, “Nan ba Amurka ba ce. Ba za ku ce saboda fararen hula na sanya kayan sojoji a Amurka, a nan ma dole ya kasance haka. Ƙari ga haka, ƙalubalen da muke fuskanta a nan, ba na tunanin suna da su a Amurka.”