✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dukan dan takara: Kotu ta sa a kamo Shugaban Karamar Hukumar Gaya

Kotun ta sa a kamo shi saboda zargin yi wa mai neman takarar kujerarsa dukan kawo wuka

Kotun Majistari da ke Karamar Hukumar Gezawa, Jihar Kano ta bayar da umarnin kamo Shugaban Karamar Gaya bisa zarginsa da lakada wa mai neman takarar kujerarsa dukan kawo wuka.

Jami’in Hulda da Jama’a na Babbar Kotun Jihar Kano, Babajibo Ibrahim ne ya sanar da umarnin da ta bayar na kamo Hon. Ahmad Abdullahi Tashi saboda dukar Hafizu Sunusi Mahmud Gaya.

Waiwaye kan musabbabin hatsaniyar

Hatsaniyar ta faru ne a lokacin da ’yan siyasa masu neman tsayawa takara a matakin kananan hukumomi ke ta fadi tashin ganin sun kai bantensu gabanin zaben da za a yi a watan Janairun 2021.

Wani ganau kuma dan uwan dan takarar, Uwaisu Sunusi Mahmoud Gaya ya ce “suna ta dukan sa har suka sumar da shi ya daina magana bayan Ahmad Tashi ya bude wa kannensa biyu kofa sun shigo suka ci gaba da dukan Hafiz”.

Uwaisu ya tabbatar wa Aminiya cewa lamarin ya auku ne a gaban kwamitin sasanta tsakanin ’yan takara da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya kafa.

An kafa kwamitin ne da nufin samar da sulhu tsakanin ’yan takarar gabanin shiga zaben fid da gwanin da za a yi a jihar.

Uwaisu ya ce, “Shugaban karamar hukumar ya bayar da umarnin duk wadanda suka zo rakiyar dan takara su ba su sarari za su shiga sulhu, sai ya tashi tsaye shi da Gamarya suka kai wa wani mai neman takarar shugabancin Gayan kuma dan yayan Sanata Gaya, Kamal Ibrahim Gaya duka.

“Daga bisani suka koma dukan Hafizu, suna ta dukan sa har suka sumar da shi ya daina magana…Da kyar muka ceci dan uwana Hafizu Sunusi daga hannunsu muka kai shi Asibitin Gaya.

“Daga baya sai Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya ya ba wa daya dan takarar, Kamal Gaya umarnin mu dawo da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano don samun kulawa sosai saboda ko magana ba ya iya yi a lokacin, har suma ya yi”, inji Uwaisu.

Tsamin dangantakar Siyasa

Gaya, karamar hukuma ce da ke da rigingimun siyasa tsakanin jagorori da mabiya.

Ana zargin dukan Hafizun ba zai rasa nasaba ba da rashin jituwar da ke tsakanin tsagin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji da tsagin dan Majalisar Tarayya mai wakilatr mazabar Gaya da Ajingi da Albasu, Abdullahi Mahmud Gaya.

Dan takarar shugabancin karamar hukumar da ya tsallake rijiya da baya dai dan yayan dan Abdullahi Mahmud Gaya ne, amma a siyasance yana biyayya ne ga tsagin Sakataren Gwamnatin Jihar da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Abdulaziz Gafasa.

Shi kuwa Shugaban Karamar hukumar tare da shugaban kansilolinsa suna bangaren dan majalisa, Abdullahi Mahmud Gaya ne.

Wani makusancin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Ibrahim Alkali, ya tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin, da cewa Usman Alhaji ya nemi Sanata gaya da Abdullahi Mahmud kan lamarin, ya kuma yi Allah wadai da abun da ya faru.