✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Duk wanda ya kara sa jarumar da ta fito daga gidan mijinta a fim wuta balbal’

Ya ce bai kamata a rika saka mata da suka fito daga gidajen aurensu a fim ba

Furodusa kuma mai wasan barkwanci na masana’antar Kannywood, Malam Habu wanda aka fi sani da Mazaje, ya yi kira da a daina sa duk wata jarumar masana’antar da ta yi aure, sannan aurenta ya mutu ta dawo masana’antar.

A wani dan karamin bidiyo da ya fitar, Mazaje ya ce, “duk wani furodusa ya sake wata ta fito a aure ya saka ta a fim, ni babu abin da zan ce masa, sai wuta balbal.”

Sannan ya rubuta a saman bidiyon cewa, “duk wata jarumar Kannywood da ta yi
aure ta fito aka sata a film, wuta balbal.”

Sai dai wani mai suna Imrana CMC ya mayar masa da martani, inda ya ce, “to kai a su wa a Kannywood? Kai da dan wasan barkwanci ne. Mazaje ba ka iya magana ba, watarana bakinka shi zai jawo a daure ka. Ka bi a hankali.”

Mazaje shi ne forodusan fim xin ‘Daga wasa’ mai dogon zango da yanzu haka ake haskawa a YouTube.