✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Duk wanda aka gani da bindiga a kamo shi —Buhari

A tsare a kuma hukunta duk mai dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba, kowaye shi.

Shugaba Buhari ya nanata umarnin tsarewa da kuma hukunta duk wanda aka samu dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba, kowaye shi.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Femi Adesina ya bayyana haka ne bayan rahoto na musamman da Daily Trust ta yi da ya nuna yawaitar makamai a hannun mutane ba bisa ka’ida ba ya taimaka wa karuwar matsalar tsaro a Najeriya.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Femi Adesina ya ce Buhari bai lamunci masu aikata muggan laifuka kuma ba ruwanshi da duk wanda aka kama da laifi ko daga wace kabila ya fito.

“Shugaban Kasa bai taba sauya matsayinsa ba na cewa a tsare duk wanda aka gani dauke da makami ba bisa ka’ida ba tare da lura da asalinsa ba,” inji shi a hirarsa da gidan talabijin na Channels.

Game da kokarin Fadar Shugaban Kasa na kawo karshen rikicin manoma da makiyaya, Adesina ya bayyana a wa shirin ‘Politics Today’ ranar Talata cewa: “An kawo wasu shawarwari da Shugaban Kasa ya riga ya yi magana a kai.

“Cigaban zamani ya sa an mamaye tsoffin burtalolin kiwo, saboda haka ya kamata a duba batun kafa gandun kiwo.

“Da farko Gwamna Ortom ma ya ce yin hakan shi ne mafita, amma daga baya ya koma yana cewa babu ai filayen da za a yi.

“Daya mafitar kuma ita ce kafa rugage, amma kuma mutane suka rika surutai cewa shi ma babu filayen da za yi.

“Yanzu kuma wasu na cewa ai tunda kiwon shanu kasuwanci ne, bai kamata gwamnati ta sa kanta a ciki ba.

“Abin tambaya a nan shi ne: Shin da gaske muna so a kawo karshen matsalar domin jin dadin kowane bangare? Abin dubawan ke na.”