Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce, zai mika wa gwamnatocin jihohin kasar dukkan jami’o’in da ke karkashin kulawar Gwamantin Tarayyar kasar idan aka zabe shi a Zaben 2023.
Atiku ya bayyana hakan ne a wajen Babban Taron Kungiyar Lauyoyin Najeriya NBA da ya gudana a Jihar Legas ranar Litinin.
- Ba ni da burin da ya wuce yi wa ’yan Najeriya hidima —Atiku
- Mutum 7 sun mutu bayan ruftawar rufin masallaci a Pakistan
Atikun na cewa kadarorin da Najeriya ta mallaka na iya karewa nan ba da dadewa ba.
“Daya daga cikin abubuwan da na shirya yi shi ne karfafa wa bangaren ‘yan kasuwa – na cikin gida da na waje – da su zuba jari a banagren ilimi domin Najeriya ba ta da kadarorin da za su dade tana sarrafa su kamar yadda take yi a yanzu.
“Na tattauna da wani malamin jami’a na Jami’ar Tarayya, Lokoja. Ya ce, ya karanta a cikin takardar manufofina cewa na yi niyyar karkata, wato in mayar da tsarin kula da ilimi hannun gwamnonin jihohi.
“Sai ya ce ta yaya zan yi hakan? “Na ce, ‘ Farfesa, ka gane cewa rukunin farko na jami’o’inmu na gwamnatocin yanki ne?’ Ya ce, ‘Eh’.
Na ce su wane ne wadanda suka gaje gwamnatin yankin? Ya ce, jahohin.“Na ce yaran da kuka tura Amurka da Ingila su waye suka mallaki wadannan jami’o’in? Galibi kamfanoni masu zaman kansu. To, me ya sa kuke tunanin ba za mu iya yi a nan ba?
Ya kuma yi tsokaci kan talaucin da ya addabi yawancin ‘yan kasar, yana cewa “tun bayan da Najeriya ta koma bisa turbar dimokradiyya a 1998/99, kasar ba ta taba samun kanta cikin tasko kamar wanda ta ke ciki ba a yanzu.”