Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta ce ta baza komarta domin ganowa da kama duk wani dan kasar waje da zai yi yunkurin kada kuri’a a babban zaben 2023 mai zuwa.
Kwanturola Janar na hukumar, Isah Jere ne ya bayyana hakan yayin wani taro na musamman kan zabe da hukumar ta shirya wa manyan jami’anta na jihohi a Abuja ranar Laraba.
- ICPC ta gano bankin da ya boye sabbin kudi na Naira miliyan 285 a Abuja
- Damisa ta kai hari a cikin kotu
Isa Jere ya kuma ce dakarunsu a shirye suke su tabbatar sun dakile duk wani yunkuri na kawo wa zaben cikas, tare da tabbatar da ’yan Najeriyar da suka cancanci zabe ne kawai suka kada kuri’a.
Kwanturola Janar din ya kuma ce hukumarsu ta sami nasarar kwace katinan zabe da na zama dan kasa daga hannun wasu ’yan kasar waje, wadanda ta ce an mayar da su kasashen waje.
Ya kuma ce sun tsaya kai da fata wajen fadakar da ’yan kasar wajen a kan illar yin zabe a kasar da ba tasu ba.
A cewarsa, “Mun yi kwararan tanade-tanade na bayar da izinin shigowa Najeriya da kuma sahalewar sanya ido a zabe ga masu neman yin haka daga ketare.”
Isa Jere ya kuma yaba wa Kwanturololin hukumar na Jihohin Kaduna da Kwara, wadanda a kwanan nan suka kama wasu ’yan kasar waje dauke da katinan zabe da na zama dan Najeriya a hannunsu. (NAN)