Duk da umarnin da Babbar Kotun Jihar Filato da ke Jos ta bayar kan rantsar da sabbin Shugabannin riko na Kananan Hukumomin Jihar, Gwamna Caleb Mutfwang ya rantsar da su a ranar Lahadi.
A baya dai, kotun, wacce ke karkashin Mai Shari’a Ishaku Kunda ke jagoranta, ta dakatar da gwamnatin jihar ta jam’iyyar PDP daga rushe Ciyamomin da ta yi daga kujerunsu.
- Abba Gida-Gida ya ci gaba da rusau a Kano
- Osimhen: Mai tallan burodi da ya zama dan kwallo mafi daraja a Afirka
An dai yi ta takun saka tsakanin Gwamna Caleb da Ciyamomin 17 kan dakatarwar da ya yi musu, inda suka ce ba ta kan ka’ida tun da dai zabarsu aka yi.
Amma Gwamnan ya ce matakin da ya dauka ya biyo bayan shawarar da Majalisar Dokokin Jihar ta bayar kan zargin da ake yi musu da yin facaka da kudaden Kananan Hukumomin nasu.
’Yan sa’o’i kafin a rantsar da sabbin Kantomomin, dakatattun Ciyamomin sun garzaya kotu inda suka nemi kotun ta hana rantsuwar, amma duk da haka Gwamnan ya yi gaban kansa wajen rantsuwar.
Yayin rantsuwar dai, Gwamnan ya sami wakilcin Mataimakiyarsa, Josephine Piyo.
Ya ce an rantsar da su ne saboda a cike gibin da aka samu na Shugabanci tun bayan dakatarwar.
Gwamna Caleb ya ce an dakatar da Ciyamomin ne bayan sun gaza gabatar da cikakkun takardun shaidu kan hada-hadar kudaden da suka yi a Kananan Hukumomin nasu.
Kazalika, Mataimakin Gwamnan ta ce dakatar da Ciyamomin ya zama dole saboda a sami cikakkiyar damar yin bincike, kuma na yi rantsuwar ce domin cike gurbin shugabanci.