✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da karin lokacin jigila, maniyyatan Najeriya 8,000 za su iya rasa Hajjin bana

Sai dai NAHCON ta ce tana da kwarin gwiwar kwashe su duka

Yayin da ya rage sa’o’i 24 karin wa’adin da Saudiyya ta yi wa Najeriya na jigilar maniyyatanta ya cika, akwai yiwuwar duk da haka maniyyata 8,000 su rasa Aikin Hajjin na bana.

Aminiya ta rawaito yadda Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita wa’adin rufe filayen jiragen saman Saudiyya da kwana biyu don Najeriya ta sami damar kwashe ragowar maniyyatanta.

Yanzu dai a maimakon Litinin din da aka tsara tun da farko, sai ranar Laraba yanzu Saudiyya za ta rufe filayen.

Sai dai duk da haka, har yanzu gwiwoyin maniyyata a sassan Najeriya sun yi sanyi sakamakon halin rashin tabbas din da suka shiga kan makomar tafiyar tasu a bana.

Har yanzu akwai maniyyata 8,000 a kasa

Binciken da wakilanmu suka gudanar sun nuna ya zuwa safiyar Litinin, kimanin maniyyata 27,359 ne aka kwasa zuwa kasar mai tsarki daga cikin 33,971 din da aka ba jihohi, ragowar 5,651 kuma har yanzu suna kasa.

Wannan adadin kari ne a kan wasu maniyyatan jirgin yawo kimanin 2,550 da su ma aka yi harsashen za su iya rasa aikin saboda kamfanonin da suka yi rajista da su har yanzu ba su biya hukumomin da suka dace a Saudiyya wasu kudade ba.

Kudaden dai su ne za su ba su damar samar musu da biza da masauki da abinci da sauransu.

Kodayake NAHCON ta ce ta tura kudaden ga Saudiyya, har yanzu akwai kamfanoni kusan 51, da ba su kai ga biyan kudaden ba.

Kowanne daga cikin kamfanonin dai NAHCON ta ba shi maniyyata 50.

A cewar Shugaban Kungiyar Masu Jiragin Yawo ta Najeriya (AHUON) Alhaji Nasidi Yahaya, akwai batutuwa masu yawa da har yanzu ba su kai ga warwarewa ba.

Ya ce, “Akwai maniyyatanmu da dama da za su iya rasa aiki na bana. Kodayake an ce akwai jiragen ko-ta-kwana da aka tanada, amma muna nan muna jiransu.

“Wasu daga cikin mambobinmu na jirgin yawo sun yi kokarin nemo canjin kudade daga kasuwannin ’yan canji, wanda bai kamata ba, duk a kokarinsu na ganin ba a sami matsala ba. Lamarin ya yi matukar muni, ba mu taba tsintar kanmu a irin wannan yanayin ba,” inji shi.

Yawan soke tashin jirage ya taimaka sosai

Sai dai hukumar NAHCON, ta bakin mai magana da yawunta, Fatima Sanda Usara, a cikin wata sanarwa ta ce Saudiyya ta yi karin kwanaki biyu ga Najeriya.

A cewar kakakin ta NAHCON, “Alkaluma sun nuna tsakanin 10 zuwa 13 ga watan Yuni, an soke tashin jirage tara saboda rashin kudaden guzuri da rashin kudaden biza da sakamakon gwajin COVID-19 da dai sauransu.

“A jimlace, an soke tashin jirage 13, sai wasu 57 da suka samu tsaiko wajen tashi. Bakwai daga cikinsu ma sai da suka sami karin kwana guda, uku kuma karin sa’o’i 23 da dai sauransu.

“Jirage 13 daga cikin 65 din da suka tashi da maniyyatan Najeriya ne kawai suka tashi babu wani tsaiko,” inji ta.

Aminiya ta rawaito cewa kamfanonin FlyNas da Max Air da Azman ne dai Najeriya ta sahalewa jigilar maniyyatan na bana.

Ana ganin yawan soke tashin jiragen maniyyata da dama sun taka rawa wajen kawo tsaikon tare da jefa su cikin halin na rashin tabbas.

Za mu kwashe duk alhazan Najeriya kafin cikar wa’adin – NAHCON 

A cewar kakakin ta NAHCON, suna da kwarin gwiwar cewa duk da tarin kalubalen, za su kwashe duk alhazan da suka cika sharudan da ake bukata kafin cikar wa’adin.

Fatima Sanda ta ce daga cikin maniyyata 43,008 da ake sa ran su yi aikin a bana, mutum 27359, ciki har da ma’aikatan hukumar 527 ne yanzu haka suka isa Saudiyyyar.

Kazalika, ta ce sama da maniyyata 5,000 daga cikin 8,097 din da aka ba ’yan jirgin yawo su ma sun isa kasa mai tsarkin.

Daga Abdullateef Aliyu Legas da Lubabatu I. Garba da Salim Umar Ibrahim da Sani Ibrahim Paki