Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu, ya ci zabe a Jihar Binuwai.
Tinubu ya lashe zabe a Jihar Binuwai ne duk kuwa da tsananin adawar gwamnan jihar, Samuel Ortom, ga jam’iyyar APC.
- Zaben shugaban kasa: Atiku ya yi nasara a Jihar Neja
- Jam’iyyu 11 sun nesanta kansu da boren PDP a wurin karbar sakamakon zabe
Ortom wanda ya ke zaman doya da manja da dan takarar jam’iyyarsa, Atiku Abubakar, ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi.
Sai dai kuma duk da haka ya gaza kai Obi ga nasara, duk da cewa kananan hukumomin da dan takarar nasa ya lashe sun fi na Tinubu yawa.
Peter Obi ya lashe kananan hukumomi uku a yayin da Tinubu ya lashe guda tara, amma duk da haka shi ke da rinjayen kuri’u.
Baturen zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Jihar Binuwai kuma Shugaban Jami’ar Kimiyya de Minna, Farfesa Farouk, ya ce, Tinubu ya zama zakara da kuri’a 310,468 a yayin da Peter Obi na LP, 308, 372, sai Atiku Abubakar na PDP da ya samu kuri’a 130,081.